Faransa na shirin sake rufe wani makeken sansanin 'yan gudun hijira
Wallafawa ranar:
Ministan cikin gidan kasar Faransa Bruno Le Roux ya bayyana aniyarsa ta ganin cikin gaggawa ya rufe sansanin bakin haure na Grande-Synthe, inda kimanin bakin haure dubu 1, 500 ke rayuwa a kusa da garin Dunkerque dake arwacin kasar.
A lokacin da yake tsokaci kan sansanin na bakin haure da suka karu ainun tun bayan lokacin da gwamnati ta rufe sansanin bayan garin Calais a watan oktoban da ya gabata, ministan cikin gidan kasar ta Fransa Bruno Le Roux, yace ba zasu taba barin lamurra su ci gaba da tafiya a yadda suke yanzu ba.
Don haka aikin tada wannan sansanin na Grande-Synthe zai fara nan bada dadewa ba.
Rikice rikicen da ake yi tsakanin ‘yan gudun hijira musamman kurdawa na ci gaba da haifar da cikas wajen tafiyar da sansanin, wanda aka kafa a cikin watan maris na 2016 a karkashin shawarar da ma’aikatar magajin garin da ta tabbatar da cewa, zata mutunta tsarin da duniya ke aiki da shi na ayukan jinkai a sansanin
Le Roux ya bayyana matukar damuwarsa kan wasu miyagun dabi’u da bakin hauren ke yi a sansanin, ga kuma uwa uba kazanta da dubban yan gudun hijirar ke rayuwa a cikin sansanin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu