An kai hari a Ofishin asusun bayar da lamuni a Paris
Wallafawa ranar:
Mutum daya ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu da aka kunshe a wasika da aka tura wa babbar cibiyar Asusun bayar da Lamuni ta Duniya IMF da ke birnin Paris na Faransa a yau alhamis.Bayan fashewar dai ne , jami’an tsaro suka bukaci jama’a su fice daga cikin ginin domin gudanar da bincike.
Hukumomin kasar sun sanar da tura yan Sanda a unguwar domin karfafa tsaro dama maida hankali wajen gudanar da bicinke a kai.
Da jimawa hukumomin na Faransa suka sanar da daukar matakan da suka dace na tsaro a birane kamar su Paris dama wajejen shakatawa.
Ya zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da bicinke domin tanttance ainayin abinda ya faru a ofishin asusun bayar da lamuni dake Paris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu