Faransa

Wani matashi ya kai hari makaranta a Faransa

Dakarun tsaro a harabar makarantar Grasse da ke Tocqueville
Dakarun tsaro a harabar makarantar Grasse da ke Tocqueville REUTERS

Jami’an tsaro sun killace wata makaranta a garin Tocqueville da ke kudu maso gabashin Faransa, bayan da aka samu musayar wuta a cikin makarantar.

Talla

Wani dalibi mai shekaru 17 ne dauke da zungureriyar bindiga ya kutsa a cikin makarantar da ke a yankin Grasse a daidai lokacin da dalibai ke daukar darasi, inda ya raunata akalla mutane 8.

Yan Sanda a kudu maso gabacin kasar na tsare da wannan matshi mai shekaru 17.
Minitan ilimi Faransa Najat Vallaud Belkacem ta kai ziyarar ba zata a wannan makaranta domin ganewa idanu ta halin da daliban suka samu kan su da kuma tattaunwa da malaman yankin ,
Minista Belkacen a zantawa da manema labarai ta bayyana cewa dalibin da ya bude wuta saman jama’a a wannan makaranta ba shida isasar lafiya, ya kasance dalibi dake sha’awar makamai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI