Faransa

An harbe wani Mahari a filin jiragen saman Orly

Jami'an tsaro sun harbe wani mutum da ya yi kokarin kai harin fillin jiragen saman Orly
Jami'an tsaro sun harbe wani mutum da ya yi kokarin kai harin fillin jiragen saman Orly Reuters 路透社

Jami’an tsaro sun harbe wani mutum da ya yi kokarin kwace bindiga daga hannu wata Soja a filin jiragen saman Orly da ke birnin Paris na Faransa.

Talla

Wannan al’amari ya ja hankali jami’an tsaro da rudani tsakanin duban matafiya da aka jibge bayan dakatar da ayyuka a tashar jirgin.

Faransa dai na cikin dari-dari tun bayan jerin hare-haren ta’addanci da aka kai mata wanda ya yi sanadi rayuka 230 a 2015.

Tuni dai aka soma bincike ta’addanci kan wannan al'amari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.