Faransa

'Yan takara sun fara Muhawara a zaben Faransa

'Yan takara a zaben Shugabancin Faransa
'Yan takara a zaben Shugabancin Faransa

A yau ne litinin 'yan takara biyar daga cikin 11 da ke neman kujerar shugabancin Faransa, za su tafka muhawara ta farko a talabijin. Muhawarar dake zuwa a dai dai lokacin da hankulan yan kasar ya rabu gani ta yadda wasu daga cikin 'yan takara sunayen su ke gaban alkalan kotu.

Talla

Daga cikin ‘yan takarar da za su shiga wannan muhawara ta farko sun hada da Emmanuel Macron, Francois Fillon,Marine Le Pen, Benoit Hamon da kuma Jean-Luc Melenchon.

Manazarta siyasar Faransa na ganin dan  takara Francois Fillon daga babbar jam’iyyar adawa wanda aka kuma bayyana cewa zai sha kaye tun a zagayen farko na zaben da za a yi a ranar 23 ga watan gobe.

Wasu sun maida hankali kan irin wainar da ake toyawa kama da tanttance 'yan takara a Zaben fitar da gwani, zuwa gwagwarmayar neman goyan bayan 'yan kasar duk da tonon silili da ake ci gaba da samu dangane da wasu 'yan takara a wannan zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.