‘Yan takarar Shugabanci Faransa za su gudanar da Mahawarar farko
Wallafawa ranar:
‘Yan takara biyar daga cikin 11 da ke neman shugabancin Faransa, za su gudanar da mahawarar farko a gidan talabijin a yammacin yau litinin.
Mahawarar na zuwa a daidai lokacin da wadanda suka fito daga manyan jam’iyyu ke kokarin farfado da kwarjininsu a idon jama’a.
Daga cikin ‘yan takarar da za su shiga wannan mahawara sun hada da Emmanuel Macron da Francois Fillon da kuma Marine Le Pen.
Sauran kuwa su ne Benoit Hamon da kuma Jean-Luc Melenchon.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta bayan-bayan nan, na nuni da cewa Francois Fillon dan takarar babbar jam’iyyar adawa zai sha kaye tun a zagayen farko na zaben da za a yi a ranar 23 ga watan gobe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu