Faransa

Faransa: An caccaki Le Pen a muhawarar farko

Shirin ‘Yar takarar shugabancin Faransa na fitar da kasar daga kungiyar kasashen Turai da kuma sukar addinin Islama ya gamu da mummunar suka a mahawarar farko da manyan ‘yan takarar zaben ksar suka yi daren jiya.

'Yan takarar Shugabancin Faransa guda 5 François Fillon da Emmanuel Macron da Jean-Luc Melenchon da Marine Le Pen da Benoit Hamon
'Yan takarar Shugabancin Faransa guda 5 François Fillon da Emmanuel Macron da Jean-Luc Melenchon da Marine Le Pen da Benoit Hamon ©PATRICK KOVARIK/AFP
Talla

Zaben shugaban kasar Faransa na sauya fasali sabanin yadda aka saba gani a shekarun da suka gabata, inda ‘yan ra’ayin rikau Marine Le Pen da Emmanuel Macron ke sahun gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a yayin da kuma ‘yan takarar manyan jam’iyyun kasar guda biyu Socialist da Republican sahun baya.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewar Macron zai doke Le Pen mai kyamar baki a zabe zagaye na biyu da za a yi ranar 7 ga watan Mayu, kuma hakan ya nuna yadda Le Pen ta yi ta shan tambayoyi kan akidun ta da ake ganin sun yi karo da manufar Faransa.

Daukacin ‘yan takarar 4 da suka fafata da Le Pen, Francois Fillon da Benoit Hamon da Jean-Luc Melenchon da kuma Macron duk sun yi ta sukar manufofinta.

Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu miliyoyin Faransawa ba su kai ga yanke hukuncin kan dan takarar da za su zaba a zagayen farko na zaben da za a yi ranar 23 ga watan gobe ba.

Ana dai danganta salon yakin neman zaben Le Pen kamar na Donald Trump na Amurka saboda yadda ta ke nuna kyamar baki tare da shan alwashin ficewa daga Tarayyar Turai idan har ta ci zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI