Birtaniya

IS ta dauki alhakin harin Birtaniya

Birtaniya na alhinin harin ta'addancin da aka kai a Westminster a birnin London
Birtaniya na alhinin harin ta'addancin da aka kai a Westminster a birnin London REUTERS

Kungiyar Daesh da ake kira IS ta yi ikirarin daukar alhakin harin ta’addancin da aka kai kusa da Majalisar dokokin Birtaniya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu cikinsu har da maharin.

Talla

Kungiyar ta bayyana maharin a matsayin daya daga cikin mayakanta, yayin da jami’an tsaron kasar suka cafke mutane takwas da ake zargi da hannu a harin.

Tuni dai Firaministar Kasar Therasa May ta lashin takobin ci ga da yaki da ta’addanci.

Jami’an ‘yan sandan Birtaniya sun kaddamar da samame, in da suka cafke mutane takwas da ake zargi da hannu a harin wanda ya jikkata mutane 40.

Mahukuntan Birtaniya sun bayyana maharin a matsayin dan asalin kasar kuma an taba alakanta shi da mai tsatstsauran ra’ayin Islama.

A jawabin da ta gabatar a gaban Majalisar dokoki, Firaministan kasar Therasa May ta ce ko kadan ba su razana ba.

Sannan ta bayyana cewa, tsarin Demokradiya ne zai ci gaba da yin nasara a kodayaushe.

May ta kuma mika godiya ga aminnan Birtaniya da suka nuna damuwa kan wannan harin.

Kimanin shekaru 12 ke nan rabon da aka kaddamnar da makamancin wannan harin a Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI