EU-Birtaniya

Dubban Jama'a sun yi zanga-zangan kin amincewa da ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai

Uwargida Theresa May Firaministan Birtaniya
Uwargida Theresa May Firaministan Birtaniya rfi

Dubban mutane ne yau Asabar suka yi maci a titunan birnin Landan don nuna kyamar neman ficewa daga kungiyar tarayyar Turai da yanzu haka Birtaniya ke ta niyya. 

Talla

Masu shirya macin na cewa mutane kusan dubu 80 suka shiga don neman kasar Birtaniya da ta zauna daram cikin kungiyar Tarayyar Turai, duk da cewa Firaministan kasar Theresa May na shirin aiwatar da janyewar kasar tun daga ranar Laraba mai zuwa.

Tun laraba data gabata aka nemi a janyen Macin saboda harin ta'addanci da aka kai Landan inda mutane 4 suka mutu, amma kuma masu shirya macin suka ki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI