Faransa

Hollande ya mayar wa Fillon martani

Shugaban Faransa Francois Hollande ya mayar da martani ga dan takarar shugabancin kasar Francois Fillon, in da ya ce, ya wuce iyaka a zarge-zargen da ya yi masa.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A ranar Alhamis din da ta gabta ne, Mr. Fillon mai shekaru 63 ya zargi Hollande da jagorantar wata tawagar sirri da ya ke ganin, ita ce ta shirya masa bita da kullin da ya kai ga tuhumar sa kan cin hanci da rashawa, abin da ya disasar da fari jininsa a wajen wajen jama’a.

To sai Mr. Hollande ya ce, ba shi da sha’awar tsoma baki a cikin muhawarar zaben kasar, amma Fillon ya wuce gona da iri.

Wanann dai na zuwa ne a yayin da ya rage kwanaki 30 a fara gudanar da zaben shugabancin kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI