Birtaniya

An kasa gano dalilin harin London

'Yan sandan Birtaniya a Wesrminster inda aka kai hari a London
'Yan sandan Birtaniya a Wesrminster inda aka kai hari a London REUTERS/Darren Staples

‘Yan sandan Birtaniya sun ce har yanzu ba su gano dalilin da ya sa aka kai hari a majalisar kasar ba wanda ya kashe mutane biyar ciki har da maharin a ranar laraba.

Talla

Yanzu ‘yan sandan sun sun saki mutane 10 daga cikin 11 da aka kama yayin da suke ci gaba da tsare da mutum guda makwabcin maharin Khalid Mosood da aka cafke a Birmingham.

Binciken ‘yan sadan ya ce maharin ya kai harin ne shi kadai, kuma yanzu bayanan asiri sun nuna babu alamun za a sake kai wani hari.

Tuni dai kungiyar IS da ke da’awar jihadi ta dauki alhakin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.