Rasha

An daure madugun adawar Rasha

Kotun Rasha ta daure madugun adawar kasar Alexei Navalny kwanaki 15 a gidan yari.
Kotun Rasha ta daure madugun adawar kasar Alexei Navalny kwanaki 15 a gidan yari. REUTERS/Tatyana Makeyeva

Kotun Rasha ta daure madugun adawar kasar Alexei Navalny kwanaki 15 a gidan yari bayan ya bijerewa umurnin ‘yan sanda na kin dakatar da jagorantar babbar zanga-zangar adawa da gwamnati.

Talla

Navalny dai na cikin daruruwan mutanen da ‘Yan sandan Rasha suka kama akan zanga-zangar kyamar Rashawa da aka gudanar a ranar Lahadi.

Kotun ta kama Navalny da sabawa doka tare da tunzura jama’a, amma lauyan da ke kare shi ta ce za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.

Wata kotu a birnin Moscow ce ta yanke wa Alexei Navalny hukuncin daurin kwanaki 15 a gidan yari a yau litinin.

Kuma alkalin da ya yanke masa hukunci Alesya Orekhova ya ci Navalny tarar kudi kimanin dala 350 kan jagorantar gangamin adawa da aka haramta a tsakiyar birnin Moscow wanda ya ja hankalin dubban ‘yan kasar.

Gwanatin Rasha dai ta zargi dan adawar da sabawa doka tare da tunzura jama’a, inda fadar shugaba Vladimir Putin ta ce an ba mutane kudi domin halartar gangamin haramtacce.

Adawa da Rashawa akan Firaministan kasar Dimtry Medvedev shi ne makusudin Gangamin da mista Navalny ya jagoranta a ranar Lahadi wanda kuma ya bazu zuwa manyan biranen Rasha.

Lauyan da ke kare Navalny, Olga Mikhailova ta ce za su daukaka kara domin kalubalantar  hukuncin daurin na kwanaki 15.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.