Birtaniya

Scotland na barazanar ficewa Birtaniya

Shugabar Scotland Nicola Sturgeon
Shugabar Scotland Nicola Sturgeon REUTERS/UK Parliament

Ana sa ran ‘Yan majalisar Scotland za su kada kuri’ar amincewa da bukatar gudanar da kuri’ar raba gardama kan ficewarsu daga Birtaniya saboda adawa da ballewa daga Tarayyar Turai.

Talla

Firaministan Birtaniya Theresa May ta roki ‘yan siyasar Scotland su jingine bukatar gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a dan samun yancin kai.

A wannan mako ne Birtaniya ke shirin kaddamar da shirin ficewa daga kungiyar kasashen Turai amma Scotland da Ireland ta Arewa na yi wa kasar barazanar ci gaba da zama a kungiyar.

Scotland da Ireland dai sun kada kuri’ar ci gaba da zama a Tarayyar Turai a kuri’ar raba gardama da aka gudanar.

Shugabar Scotland Nicola Sturgeon ta ce an tursasa ma su ficewa daga Tarayyar Turai bayan ta gana da Firaminista Thareza May a jiya Litinin.

Scotland na fatar gudanar da kuri’ar raba gardama a 2019 kafin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.