Birtaniya-EU

Birtaniya ta mika wasikar ficewa daga Turai

Shugaban zantarwar Tarayyar Turai Donald Tusk ya karbi wasikar ficewar Birtaniya
Shugaban zantarwar Tarayyar Turai Donald Tusk ya karbi wasikar ficewar Birtaniya REUTERS/Yves Herman

Birtaniya ta mika wasikar ficewarta ga mahukuntan Kungiyar Kasashen Turai a wannan Laraba don ci gaba da shirin kawo karshen zamanta na shekaru 44 a cikin kungiyar a hukumance.

Talla

A yau ne Firaministar Birtaniya Therasa May ta gabatar da jawabi ga mambobin Majalisar Dokokin kasar, in da ta sanar da su cewa ta aiwatar da doka ta 50 da ke kunshi a yarjejeniyar kungiyar Tarayyar Turai.

A halin yanzu dai Birtaniya na sa ran kammala ficewarta baki daya daga Turai nan da shekaru biyu masu zuwa.

Kimanin watanni tara kenan da al’ummar Birtaniya suka kada kuri’ar ficewa daga kungiyar kasashen Turai, abin da ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.