Birtaniya

Birtaniya zata kaddamar da shirin ficewa daga EU

Friministan Britaniya Theresa May
Friministan Britaniya Theresa May REUTERS/Leon Neal

Yau ake saran Birtaniya a hukumance zata kaddamar da shirin ficewa daga kungiyar kasashen Turai, mataki na farko da ya raba kan al’ummar kasar da kuma makomar kungiyar.

Talla

Kwanaki bayan cika shekaru 60 da kafuwa, Birtaniya zata zama kasar ta farko wadda zata fice daga kungiyar, watanni 9 bayan gudanar da zaben raba gardamar da ya amince da shirin.

Ana saran Firaminista Theresa May zata shaidawa 'Yan Majalisu muhimmancin dogaro da kai ganin yadda 'yan kasar suka zabarwa kan su makomar da suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI