Amurka

Kotu ta tsawaita dakatar da dokar hana baki shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Wata kotu a jihar Hawaii karkashin Alkali Derck Watson, ta tsawaita dakatar da dokar hana shigar baki kasar daga kasashen Musulmi 6, da shugaba Donald Trump ya sanyawa hannu.

Talla

Hawaii da wasu Jihohin Amurka sun bayyana dokar ta shugaba Trump, a matsayin wadda ke da nasaba da addini, kuma wadda tayi karo da manufar Amurka a matsayin kasa mai mutunta dukkanin bangarorin jama’a.

Ana saran nan da wani lokaci ma’aikatar shari’ar Amurka ta daukaka kara kan wannan hukuncin.

Wasu ga cikin kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin da adam suna cigaba da sukar dokar ta Trump a matsayin wadda aka nufa da kuntatawa Muslmi kawai, batun da shugaban Amurkan ke cigaba da musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.