Isa ga babban shafi
Faransa

Tattaunawar kawo karshen zanga-zanga a Guyane

Ministan dake kula da tsibiran Faransa Ericka Bareigts a Guyane
Ministan dake kula da tsibiran Faransa Ericka Bareigts a Guyane jody amiet / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

An soma tattaunawar neman mafita a zanga zangar da ta barke a Guyane, daya daga cikin tsibiran utr-mer dake karkashin kasar Faransa.Gwamnatin Faransa ta tura da ministan dake kula da tsibiran Ericka Bareigts wanda ya nemi gafarar mutan tsibirin da suka bukaci kara inganta rayuwarsu kamar na sauran yankunan kasar ta Faransa. 

Talla

Talakawa masu zanga zangar na bukatar ganin gwamnatin Faransa ta dau halin da suke ciki da muhimmanci, musaman wajen magance matsalar talauci da rashin aikin yi da ake fama da shi.
Yanzu haka zababbun yankin sun gabatar da bukatun magancewa al’ummominsu matsalolin da suke fama dasu ga yan takarar shugabancin kasar.

Kudaden shiga da na harajin da yankunan ke samu domin gudanar da ayyukan ci gaban rayuwar jama’a sun kankance a ya yin da kudaden da gwamantin faransa ke ware masu kuma suka yi kasa

Gwamnatin Faransa ta sanar da ware kusan bilyan daya na euro a matsayin tallafi,shawarar da masu zanga-zangar suka nuna adawa a kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.