Turai

'Yan majalisun turai zasu dauki mataki kan gurbatar iska da motoci ke haifarwa

Kamfanin Volkswagen ya amince da zargin da aki masa na sanya wata na'ura a motocin da ya kera a shekara ta 2015 cikin akalla injinan motocindsa miliyan don kaucewa binciken sa ido kan hayakin da motocinsu ke fitarwa.
Kamfanin Volkswagen ya amince da zargin da aki masa na sanya wata na'ura a motocin da ya kera a shekara ta 2015 cikin akalla injinan motocindsa miliyan don kaucewa binciken sa ido kan hayakin da motocinsu ke fitarwa. phys.org/news

‘Yan majalisun kasashen Turai sun bukaci Gwamnatocin yankin su gaggauta kafa hukumar da zata rika sa ido kan yadda kamfanonin hada motoci ke zamba, wajen gwajin hayakin da motocin da su ke kerawa ke fitarwa, bayan gano matsalar da kamfanin Volkswagen ya samu.

Talla

Majalisar tace a cikin shekaru 10 da suka gabata sun gano cewar hayakin da ake fitowa ya zarce wanda ake bayyanawa a dakin bincike.

Majalisar ta kuma bukaci kamfanonin hada motocin su biya diyya ga mutanen da hayakin ya yiwa illa.

A gefe guda, dangane da matsalar gurbacewar isaka da ke haddasa mutuwar mutane dubu 9000 a ko wace shekara a birnin Landon, Magajin garin birnin Sadiq Khan, ya bayyana kebe wani yanki na birnin da zai kare daga matsalar, a shekarar 2019, ta hanyar daura damarar yaki da motocin dake gurbata yanayi.

Sabon matakin zai shafi dukkanin motocin dake amfani da makamashin man Gaz masu shekaru 4 da kerawa, da kuma masu shekaru 13 dake amfani da Fetur, wadanda zasu dinga biyan haraji mai tsoka, don samun damar yin zirga zirga a tsakiyar birnin Landon a ko wane lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.