Sweden

Direba ya kusta babbar mota a cikin taron jama’a

Kafar yada labarai a Stockholm ta soma nuna hotunan harin da ake tunanin na ta'addanci ne.
Kafar yada labarai a Stockholm ta soma nuna hotunan harin da ake tunanin na ta'addanci ne. France24

Wani mutum ya kutsa da babbar mota a cikin taron jama’a a tsakiyar birnin Stockholm na kasar Sweden, kawo yanzu ‘yan sanda sun tabbatar da cewa mutane da dama ne aka tabbatar da cewa sun samu rauni sakamakon taka su da aka yi da mota, inda suka ce sun fara bincike a game da lamarin.

Talla

Ba’a dai iya tantance harin ko na ta’addanci bane sai dai Firaiministan Sweden Stefan Lofven ya ce ga dukkan alamu harin na ta’addanci ne aka kawo a kasar.

Shugabanin kasashen duniya na ci gaba da yin Allah-wadai da wannan al’amari da yanzu haka ya matukar girgizar al’ummar kasar.

Yin anfani da mota wajen kai hare-haren ta'addanci ya soma zama ruwan dare gama gari a kasashen Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.