IMF-Amurka

IMF ya musanta samun tsamin dangantaka tsakaninsa da Amurka

Shugabar Asusun bada lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde
Shugabar Asusun bada lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde REUTERS/Hannibal Hanschke

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya ce tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamnatin Donald Trump ba kai yadda wasu ke yayatawa a duniya ba. 

Talla

Shugabar asusun Christine Lagarde ta ce ganawar da ta shiga tsakaninta da hukumomin gwamnatin Amurka zuwa yanzu, ta bata gwarin gwiwar kafa hujjar cewa za’a samu cigaba.

Bayanin na Largarde ya zo ne kafin taron mambobin asusun bada lamunin guda 189 da za’a yi a birnin Washington cikin wannan makon.

A baya asusun na IMF ya bayyana fuskantar kalubale da gwamnatin Amurka kan wasu manufofinta, da ya hada da hada hadar kasuwaci da kudade.

A wannan makon sakataren harkokin kasuwancin Amurka Wilbur Ross ya yi watsi da wasu batutuwan asusun da ya dangata da shirme, kana kasar ta bukaci asusun ya fi bada karfi ga kasashen dake karkashinsa, ya kuma kauracewa tsare-tsaren da zai cutar da Amurka.

Sai dai a martaninta, hugabar asusun na IMF Christine Lagarde ta ce, asusun na gudanar da ayyukansa ne kan tsari ba tare da jefa kowa cikin kunci ba.

Lagarde ta kuma kara da cewa IMF ba kungiyar kasuwanci ba ce, sai dai ta kan nuna damuwarta kan kasuwanci domin shi ne ginshikin samar da ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.