Faransa

Le Pen ta yaudari Majalisar Turai

Marine Le Pen, 'Yar takarar Jam'iyyar FN masu kishin kasa a Faransa
Marine Le Pen, 'Yar takarar Jam'iyyar FN masu kishin kasa a Faransa REUTERS/Eric Gaillard

Sakamakon wani binciken ya bankado cewa jam’iyyar Front National ta Marie Le Pen masu zazzafan ra’ayin rikau a Faransa ta zanbaci majalisar Tarrayar Turai kudadden da yawansu ya kai Yuro miliyan 5.

Talla

An gano cewa akwai yiyuwar ‘yar takarar kujerar shugabancin Faransa ta zambaci Majalisar wadannan kudadden tare da wasu na hannun damanta a jam’iyyar Front National da ta ke shugabanta.

Jam’iyyar FN dai na da ‘Yan Majalisa da yawansu ya kai 24.

Majalisar Turai na zargin kudaden sun tafi asusun wasu Jami’an Jam’iyyar FN da ba su aiki a Majalisar.

Yanzu haka masu bincike a Faransa sun kaddamar da bincike game da badakalar. Amma Jam’iyyar ta Le Pen ta fito da musanta zargin.

A ranar 7 ga watan Mayu ne Le Pen za ta fafata da Emmanuel Macron a zaben shugaban kasa zagaye na biyu. Ana ganin binciken baraka ne ga yakin neman zabenta
Le Pen dai ta sha alwashin fitar da Faransa daga cikin Kungiyar Tarayyar Turai idan har ta ci zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.