Faransa

Masu kishin kasa sun samu koma-baya a Turai

Marine Le Pen da ta sha kayi a hannun Emmanuel Macron a zaben shugabancin Faransa
Marine Le Pen da ta sha kayi a hannun Emmanuel Macron a zaben shugabancin Faransa AFP PHOTO / KIRILL KUDRYAVTSEV

Masharhanta sun bayyana kayin da Marine Le Pen ta sha a zaben shugabancin Faransa a matsayin sabon koma-baya ga masu tsattsauran ra’ayi kishin kasa a nahiyar Turai. Wannan na zuwa ne bayan masu kishin kasan sun sha irin wannan kayin a Austria da Holland, abin da ke nuna cewa, har yanzu akwai sauran aiki a gabansu.

Talla

Uwargida Marine Le Pen mai kishin kasa ta yi fatan samun nasara a zaben Faransa zagaye na biyu don kammala aikin da mahaifinta ya gaza kammalawa a shekarar 2002, loakcin da shi ma ya sha kayi a zagaye na biyu na zaben kasar.

Le Pen na da ra’ayin janye Faransa daga kungiyar kasashen Turai kuma a yakin neman zabenta ta mayar da hankali kan batun shige da ficen baki da kuma baranazar ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare.

Sai dai burin Le Pen na raba Faransa da EU ya gamu da cikas, abin da masu kishin kasa ke kallo a matsayin koma-baya a gare su.

Emmanuel Macron da ke goyon bayan zaman Faransa a EU ne ya lashe zaben na ranar Lahadi da kashi 66 cikin 100, yayin da Marine Le Pen ta samu kashi 34.

Wannan sakamako dai shi ne irinsa na uku a cikin watanni shida da ke nuna rashin nasara ga masu tsattsauran ra’ayi a Turai.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Disamban bara ne Nobert Hofer mai tsattsauran ra’ayi a Austria ya sha kayi a zagaye na biyu na zaben kasar.

Sannan kuma a cikin watan Maris da ya gabata, Geert Wilders mai adawa da Islama ya gaza kai ga gaci a zaben Holland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.