NATO

NATO za ta shiga yaki da IS a Syria da Iraqi

Dakarun kungiyar tsaro ta NATO
Dakarun kungiyar tsaro ta NATO Reuters

Kungiyar tsaro ta NATO za ta shiga yakin da Amurka ke jagoranmta akan Mayakan IS, a Syria da Iraqi. matakin na zuwa kafin ganawar da shugaban Amurka Donald Trump zai yi da shugabannin mambobin kungiyar NATO a Brussels a ranar Alhamis.

Talla

Wasu majiyoyin difolamsiya ne suka tabbatar da cewa NATO za ta shiga yakin da Amurka ke jagoranta akan mayakan IS, bayan Trump ya bukaci kungiyar tsaron ta mayar da hankali ga yakar ayyukan ta’addanci.

Tuni sakararen harakokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana fatar ganin NATO ta shigo cikin yakin da Amurka ta kaddamar akan IS duk da wasu mambobin kungiyar na dari dari da abkawa cikin wani yaki a yanzu.

Wasu majiyoyi daga Turai sun ce Faransa da Jamus sun amince da kudirin na Amurka kan shigowar NATO a yaki da IS a ganawar da Trump zai yi da shugabannin kasashen na Turai

Rahotanni sun ce Jekadun kasashen mambobin NATO sun tsara matakan yaki da ta’addanci a taron da shugabannin na Turai za su yi da Donald Trump.

Matakan kuma sun hada da fadada ayyukan jiragen leken asiri na NATO wajen yakar IS a Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.