Faransa

Sabuwar dokar hana 'yan majalisa daukar iyalansu aiki a Faransa

François Bayrou, Ministan shari'ar kasar Faransa
François Bayrou, Ministan shari'ar kasar Faransa RFI/ Pierre René-Worms

Gwamnatin Faransa, ta sanar da shirin kafa dokar haramta wa wakilan majalisar kasar daukar iyalansu ayyuka, wannan kuwa a matsayin tsaftace siyasar kasar.

Talla

Ministan Shari’ar Faransa Francois Bayrou ya ce burin gwamnati shi ne dawo da martabar masu rike da mukaman siyasa a idanun al’ummar kasar.

Kari daga cikin kudurori 10 da sabuwar dokar zata kunsa, kamar yadda ministan shara’a Bayrou ya bayyana cewa akwai tanadin haramta wa masu neman mukaman siyasa da aka taba yankewa hukunci kan aikata kanana ko manyan laifuka masu alaka da almundahana,tsayawa takara tsawon shekaru 10.

Sai kuma cewa daga yanzu dole ne dukkanin ‘yan majalisar kasar ta Faransa, su gabatar da rasitan bankunan kudaden da suka yi amfani da su wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum da suka shafi ayyuka, ba kamar yadda tsarin yake da ba, inda ake ba su makudan kudade kai-tsaye ba tare da bin kadi ba.

Yunkurin na zuwa ne bayan bankado badakalar da aka samu tsohon firaministan Faransa Francois Fillon dumu-dumu ciki na bai wa matarsa Penelope makudan kudaden alabashi kan aikin da bata yi ba, a majalisa, lamarin da ya taimaka kan kayan da ya sha a zaben shugabancin kasar da ya gudana a watan Afrilu da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.