Faransa

Faransawa na shirin zaben 'yan majalisa a ranar lahadi

Emmanuel Macron, shugaban Faransa
Emmanuel Macron, shugaban Faransa REUTERS/Charles Platiau

A ranar lahadi mai zuwa za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a Faransa, zaben da ke matsayin babban kalubale ga shugaban kasar Emmanuel Macron wanda ke fatan samun rinjaye a cikin zauren majalisar.

Talla

Akwai dai jam’iyyun da dama da suka tsayar da ‘yan takara a wannan zabe wanda za a yi zagaye na farko a ranar 11 yayin da za a yi zagaye na biyu a ranar 18 ga wannan wata, bayan da Faransawa da ke zaune kasashen ketare suka gudanar da nasu zaben a karshen makon jiya.

Manazarta dai na kallon zaben na ‘yan majalisa a matsayin babban kalubale ga jam’iyyar La Republique en Marche ta shugaba Emmanuel Macron, yayin da wasu ke cewa tsoffin jam’iyyun da ake da su a kasar irinsu les Republicains, da Socialiste ko kuma Front National ne suka fi fuskantar kalubale, lura da kayen da suka sha a zaben shugabancin kasar na watan jiya, wanda bai kamata su sha makamancinsa ba a wannan karo.

Idan har sabuwar jam’iyyar ta La Republique en Marche ta samu rinjaye a zaben na jibi, hakan zai kasance mummunan koma-baya ga tsoffin jam’iyyun da suka mamaye fagen siyasar kasar ta Faransa tsawon shekaru.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya-bayan nan wadda cibiyar nan mai suna Ipsos Sopra Steria ta fitar, na nuni da cewa jam’iyyar Macron ce za ta kasance jagora da kashi 29 cikin dari, sai Les Republicains da kashi 23, Front national mai 17 %, sai Socialist a matsayin ta 5 da kujerun da ba za su wuce kashi 8 cikin dari ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.