Faransa

'Yan adawar Faransa na fargabar mika rinjaye ga Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Philippe Wojazer

‘Yan adawar Faransa sun gargadi mika rinjayen Majalisar Dokokin kasar ga jam’iyyar shugaba Emnmanul Macron, abin da suka ce zai hana zazzafa muhara a zauren Majalisar.

Talla

‘Yan adawar sun yi gargadin ne bayan Jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron da aka kafa ta shekara guda da ta gabata, da sauran kawayenta sun kama hanyar lashe kimanin kujeru 445 daga 577 a Majalisar kasar.

‘Yan adawar da jaridun Faransa sun nuna damuwa kan wannan sakamakon, lura da cewa hakan zai rage tagomashin siyasar kasar.

Shugban ‘yan adawa a jam’iyyar Republican shiyar Paris, Valerie Pecreasse ya gargadi matsalar da aka iya biyo baya sakamakon shawarar da bangare daya zai rika yanke wa a Majalisar.

Zaben ‘yan Majalisun da aka gudanar a karshen mako, ya rasa tagomashi saboda karancin jama’ar da suka fito don kada kuri’unsu.

Bayan kayin da suka sha a zaben shugabancin kasar, manyan Jam’iyyun Republican da Socialist sun sake shan mummunan kayi a zaben na karshen mako duk da cewa sun shafe shekaru 60 suna musayar mulki a tsakaninsu.

Sai dai Jam’iyyun guda biyu sun bukaci Faransawa da su fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’u a zagaye na biyu wanda za a yi a ranar 18 ga wannan wata, yayin da suka gargade su game da mika ragamar Majalisar kasar ga Jam’iyya guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.