Faransa

La Republique en Marche ta samun rinjaye a zaben Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayinda yake shirin zuwa rufar zabe, a zagayen zaben 'yan majlaisar kasar karo na farko ranar 11  ga watan Yuni.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayinda yake shirin zuwa rufar zabe, a zagayen zaben 'yan majlaisar kasar karo na farko ranar 11 ga watan Yuni. REUTERS/Philippe Wojazer

A kasar Faransa an kamala zaben ‘yan majalisar dokoki zagaye na biyu a wannan lahadi, inda Jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron La Republique en Marche ta samun rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar.

Talla

J'am'iyyar 'La Republique en Marche' ta Macron, da ta bata wuce shekara guda da kafuwa ba, ta samu rijaye na kuri'un da aka kada, wato tsakanin kujeru 355  daga cikin jimillar kujerun ‘yan majalisun kasar 577.

Wannan nasara ta shugaban kasar na bashi damar samun rijaye a  majalisar kasar Faransa, karo na farko, da aka samu gagarumin sauyin gwamnati a Faransa, tun bayan wanda aka gani a shekarar 1958, lokacin da kasar ta fara amfani da tsarin dimokaradiyya na shugaban kasa mai cikakken iko.

'Yan adawa a Faransa, sun fara bayyana fargabar su, da cewa wannan nasara ta Shugaban kasar barazana ce  ga dimokaradiyyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.