Faransa

Macron ya samu rinjaye a Majalisar Faransa

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Bertrand Guay/Pool

Jam’iyyar shugaban Emmanuel Macron, La Repubulipue en Marche ta samu gagarumin rinjaye a zaben ‘yan majalisar dokoki zagaye na biyu da aka gudanar ranar Lahadi a kasar Faransa.

Talla

Sakamakon zaben ya nuna cewa jam’iyyar shugaban kasar da kuma sauran kawayenta za su tashi da kujeru 355 daga cikin 577 da ake da su a zauren majalisar dokokin kasar.

Cibiyar Ipsos wadda ta tattara sakamakon zaben jim kadan bayan kammala jefa kuri’a, ta ce babbar jam’iyyar adawa ta Les Republicains za ta tashi ne da kujeru 125, yayin da jam’iyyar Socialist ta tsohon shugaba Francois Hollande da masu ra’ayi irin nata za su samu kujeru 49.

Sai dai karon farko a tarihi jam’iyyar masu zazzafen ra’ayin kishin kasa National Front a karkashin jagorancin Marine Le Pen ta samu wakilai 8 a cikin zauren majalisar dokokin kasar ta Faransa.

Wannan sakamako dai babbar nasara ce ga Emmanuel Macron, wanda ke fatan samun damar aiwatar da sauye-sauye da dama a fagen siyasa da tattalin arziki da kuma na zamantakewar al’ummar Faransa kamar yadda ya alkawanta a lokacin yakin neman zabensa.

Alkaluma sun nuna, an samu karancin fitowar jama’a a zaben 'Yan Majalisun.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.