Faransa

An fara binciken Marine Le Pen a Faransa

Uwargida Marine Le Pen, shugabar jam'iyyar National Front a Faransa
Uwargida Marine Le Pen, shugabar jam'iyyar National Front a Faransa 路透社

Masu shigar da kara na Faransa sun fara binciken shugabar Jami’iyyar National Front mai tsattsauran ra’ayi Marine Le Pen a hukumance, bisa zargin ta da barnatar da kudaden Majalisar Dokokin Tarayyar Turai.

Talla

Ana zargin Le Pen da yin amfani da kudaden Majalisar wajen biyan wasu kananan ma’iakatan Jam'iyyarta a Faransa, abin da aka danganta da cin amana.

Sai dai Uwargida Le Pen ta sha musanta aikata ba dai dai ba, in da ta ke cewa, ana yi ma ta bita da kullin siyasa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Lauyanta ya ce, za su daukaka kara don kalubalantar matakin binciken ta.

A wannan Juma’ar ce, Uwargida Le Pen ta bayyana a gaban kotu duk da cewa, a can baya ta yi watsi da kiran da kotun ta yi ma ta a dai dai lokacin da ta mayar da hankali kan yakin neman kuri’u a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.

Kazalika ana binciken Le Pen game da yada hotunan mayakan ISIS a shafinta na Twitter, in da ta nuna irin ta’asar da mayakan ke yi, abin da ya janyo ma ta caccaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.