Turai

Shugabannin Turai Sun Yi Juyayin Marigayi Helmut Kohl NA Jamus

Marigayi Helmut Kohl,cikin wani hoto a shekara ta 2010
Marigayi Helmut Kohl,cikin wani hoto a shekara ta 2010 REUTERS/Kai Pfaffenbach

Shugabannin kasashen Turai tare da tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton sun hadu yau a birnin Strasbourg don bukin Juyayin tsohon  Shugaban Gwamnatin Jamus Marigayi Helmut Kohl, wanda ake yiwa ikirari da Uba da ya hada kawunan Jamusawa.

Talla

Shugaban Hukumar Kasashen Turai Jean-Claude Juncker ya bayyana marigayi Helmut Kohl da cewa jagora ne abin koyi, inda yake cewa mutun ne mai kishin Jamus, kuma yana kaunar kasashen Turai.

Shi dai Helmut Kohl ya jagoranci Gwamnatin  Jamus tsakanin shekara ta 1982 zuwa 1998, kuma ya mutu ne ranar 6 ga watan daya gabata na Yuni ya na da shekaru 87.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.