Faransa

Dan bindiga ya bude wuta kusa da Masallaci a Faransa

An taba kai hari a Masallacin Créteil, da ke Paris a Faransa
An taba kai hari a Masallacin Créteil, da ke Paris a Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes

Wani dan bindiga ya buda wuta tare da raunata mutane 8 a kofar wani masallaci da ke garin Avignon da ke kudancin Faransa, al’amarin da mai shigar da kara na gwamnati ya nisanta da ayyukan ta’addanci.

Talla

‘Yan sanda sun ce da misalin karfe 10 da rabi na daren jiya ne wasu mutane biyu cikin wata mota suka buda wuta a kofar masallacin, inda yanzu haka ake ci gaba da farautar maharan.

Harin na zuwa kwanaki bayan wani mutum ya abka wa masu ibadah a masallacin Cretail kudancin Paris a ranar Alhamis.

Al’ummar musulmi a Faransa sun bayyana damuwa akan yadda ake kokarin kai masu hari a wajen ibadah inda suka yi kira ga mahunkunta wajen tabbatar da tsaro musamman a masallatai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.