Faransa

Macron ya bayyana bukatar rage yawan 'yan majalisu

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin da yake jawabi a gaban zauren majalisar kasar.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin da yake jawabi a gaban zauren majalisar kasar. Eric FEFERBERG / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da bukatar zaftare kashi daya bisa uku na yawan ‘yan majalisun kasar, a bangaren dattawa dana wakilai.

Talla

Macron ya bayyana matakin yayinda yake gabatar da jawabi a zauren majalisar, inda ya kare aniyar tasa da cewa, hakan zai takarawa wajen inganta ayyukan bangarorin majalisar dattawan da na ‘yan wakilan.

A cewar Macron mataki ne da ‘yan kasa suka shafe tsawon lokaci suna fatan ganin ya tabbata, wanda ya zamewa gwamnatinsa wajibi ta tabbatar da aiwatar da shi.

Bangaren zauren majalisar dattawan na da wakilai 348 yayinda majalisar wakilan ke da kujeru 577.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.