Turai

Masu fautuka sun lashi takobin gudanar da zanga zanga a Hamburg

Dubban masu fafutuka da suka lashi takobin adawa da taron kasashen G20
Dubban masu fafutuka da suka lashi takobin adawa da taron kasashen G20 France24

Daruruwan masu fafutuka da ke adawa da kasashe 20, masu karfin tattalin arziki na G20, sun sha alwashin ci gaba da shirin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da taron kasashen, duk da barazanar jami’an ‘yan sanda na hana su kafa tantuna a birnin Hamburg na kasar Jamus.

Talla

Yunkurin zanga-zangar dai ya zo kwanaki kadan gabanin fara babban taron kasashen na G20 da zai gudana a kasar ta Jamus.

Tuni dai jami’an ‘yan-sanda suka dakile yunkurin masu fafutukar sama da 600 wadanda ke shirin kafa tantuna a birnin Hamburg da ke Jamus, lamarin da ya kai ga jikkatar mutum guda.

Akwai da tunanin cewa masu fafutukar za su gudanar da zanga-zangar wurare daban daban har guda 30 kafin, bayan, da kuma a lokacin da ake tsaka da taron na kwanaki biyu wanda za a fara ranar Juma’ar Makon nan, lamarin daya haddasa girke kimanin jami’an ‘yan-sanda dubu 20 don bada kariya.

Tun a makwannin da suka gabata ne dai masu shirya zanga-zangar da kuma mazauna arewacin birnin na Hamburg ke fafutukar ganin sun samu damar kafa isassun tantuna masu dauke da makewayi da kuma dakunan girki don amfanin mutanen da za su fito, ta hanyar tuntubar kotuna don samun izini.

Sai dai kuma a cewar kotunan umarnin kafa tantunan ba zai tasiri ba la’akari da cewa jami’an ‘yan-sanda nada ikon dakile lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.