Turkiya

Majalisar Turai ta amince a jingine bukatar Turkiya

Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan REUTERS

Majalisar dokokin Tarayyar Turai, ta bukaci a kawo karshen duk wata tattaunawa da Turkiya dangane da yunkurin kasar na zama mamba a kungiyar, sakamakon adawa da majalisar ke yi da gyaran kundin tsarin mulkin kasar da ya kara karfin iko ga shugaba Racep Tayyip Erdagon.

Talla

A kuri’ar da aka jefa a jiya Alhamis ‘yan Majalisa 477 ne suka goyi bayan matakin katse tattaunawar, yayin 64 suka nuna adawarsu.

Kudurin dai ya bukaci a dakatar da duk wata tattaunawa da Turkiya idan har kasar ta tabbatar da kundin tsarin mulkin da aka yi wa kwaskwarima.

A watan Mayu, shugaba Erdogan ya ce ba zai koma yana bara ba, yanzu ya rage ga Tarayyar Turai ya yanke shawara akan bukatar kasarsa na zama mamba a kungiyar.

Daga cikin sabbin dokokin da kasashen Turai ke adawa da su a kundin tsarin mulkin sun hada batun dawo da hukuncin kisa a Turkiya inda kasashen ke son a zauna domin fahimtar juna kafin karshen shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.