Italiya

An tattauna yadda za a dakile kwararar ‘yan ci-rani zuwa Turai

Ministocin harkokin wajen kasashen Turai da Afirka sun kammala wani taro kan yadda za a tunkari matsalar kwararar bakin haure da ke tasowa daga Libya zuwa Turai.

Dubban mutanen Afrika ne a kullum ke tsallaka tekun Bahrum zuwa Turai
Dubban mutanen Afrika ne a kullum ke tsallaka tekun Bahrum zuwa Turai REUTERS
Talla

Ministocin harkokin wajen Libya da Nijar da Tunisia da Masar da Chad, Habasha da Sudan ne suka wakilci Afirka a taron tare da takwarorinsu na Turai da suka kunshi na kasashen Jamus da Austria da Spain da Faransa da Holland da Malata da Estonia.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, ya ce matsala ta farko da ya kamata a tunkara ita ce matsalar kasar Libya, lura da irin halin da kasar ke ciki.

Ya ce za su fi mayar da hankali ne kan abin da ya fi damuwar kasashen Turai baki daya ba wai abin da ya shafi Faransa da Italiya kawai ba.

“Ya kamata mu yi kokarin samar da mafita ga rikicin da kasar ke fama da shi, wanda shi ne babban dalilin matsalar kwararar bakin haure”a cewar Le Drian, .

Sannan ya ce ya zama wajibi a tallafa wa kasashen da ke mokwabtaka da Libya ta bangaren kudu, kamar Nijar da kuma Mali, musamman ta fannin tsaro.

Taron ya tattauna yadda za a taimaka wa kasashen Afirka ta fannoni da dama da sake fasalta tsarin samar da takardar biza da kuma tsara yadda za a mayar da bakin haure zuwa kasashensu.

Italiya ta ce ta ware kudi yuro miliyan 10 ga Libya domin kare iyakokinta da Nijar da Chad da Sudan, kasashen da ake ratsowa zuwa cikin kasar da nufin tsallakawa zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI