Bakin-haure

Bakin haure da ke shiga turai ta Spain sun rubanya

Bakin haure na sauya hanyar shiga Turai ta Libya
Bakin haure na sauya hanyar shiga Turai ta Libya ReutersREUTERS/Stefano Rellandini/File photo

Alkaluman Bakin haure da ke Isa gabar ruwan kudancin Spain sun rubanya a shekarar 2017 sakamakon kauracewa bi ta Libya da ke fama da rashin zaman lafiya don isa nahiyar Turai.

Talla

Jirage 8 dauke da Mutane 380 aka ceto a cikin wannan makon a tekun Alboran, wanda ya hada arewa maso gabashin Moroko da Kudancin Spain, a yammacin Mediterranean.

Kungiyar SOS da ke Karin Hakkin dan adam a Spain, tace alkaluman abin damuwa ne da ba a saba gani ba duk da matakan da ake dauka.

A ko da yaushe ana sake samun karuwar Bakin haure da ke mutuwa a kan teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.