Turai

Kotu ta haramta sanya hijabi a Turai

Nau'in hijibi ko kuma nikabi da kotun Turai ta haramta sanyawa a bainar jama'a
Nau'in hijibi ko kuma nikabi da kotun Turai ta haramta sanyawa a bainar jama'a REUTERS/Gonzalo Fuentes

Babbar Kotun kare hakkin bil Adama ta kasashen Turai ta amince da hukuncin haramta hijabin da ke rufe daukacin fuskar mata a bainar jama’a. Matakin ya biyo bayan korafin da wasu mata biyu Musulmai suka shigar, in da suke korafin cewar haramta amfani da hijabin ya saba wa addinin Islama.

Talla

Kotun ta ce dokar hana amfani da hijabin da ke rufe daukacin fuskar mace, an kafa ta ne domin karfafa danganta a cikin al’umma da kare hakkokin jama’a a kasar da ke bin tafarkin dimokiradiya.

Kotun ta ce dokar da aka amince da ita a cikin watan Yuni na shekarar 2008 a yankuna 3 na kasar Belguim, za ta taimaka wajen kare hakkokin jama’a na zaman tare ba tare da musguna wa juna ba.

A shekarar 2011, kasar Belgium ta amince da dokar ta bai daya a fadin kasar, wadda ke dauke da hukuncin tara da kuma daurin kwanaki 7.

Faransa ce kasa ta farko da ta fara haramta amfani da irin wannan hijabin a watan Afrilun shekarar 2011, kuma kotun Turai ta yi watsi da cewa dokar ta karya ka’idojin addinin Islama.

Wasu mata biyu Musulmai 'yan kasashen Belguim da Morocco ne suka shigar da karar, in da suke kalubalantar haramta amfani da hijabin da ke lullube fuska baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI