Faransa

Attajiran Faransa za su fi more tsarin harajin Macron

Emmanuel Macron, shugaban Faransa
Emmanuel Macron, shugaban Faransa REUTERS/Christian Hartmann

Gwamnatin Faransa ta ce zuwa badi zata datse harajin kasuwanci da kuma wanda mutane ke biya da kusan yuro biliyan 11. Firaminitan kasar ne ya tabbatar da matakin, wanda za a aiwatar cikin gaggawa sabanin lokacin da gwamnatin ta yi alkawali.

Talla

Manufar Gwamnatin Macron dai shi ne kara bude hanyoyin saka jari da samar da ci gaba ga habakar tattalin arziki.

Tun a yakin neman zabensa shugaba Macron ya yi alkawalin datse harajin kudi kimanin biliyan 20 na yuro a shekaru 5.

Daga cikin fannonin da za a datse harajin sun hada da datse kashi 80 na harajin da mazauna gari ke biya da datse harajin da attajirai da kamfanoni ke biya.

Wannan dai duk mataki ne da ake ganin zai kara janyo hankali masu saka jari a Faransa.

Sai dai kuma wani Bincike ya nuna cewar shirin shugaba Emanuel Macron na zabtare harajin da jama’a ke biya a kasar zai fi taimakawa kashi 10 na attajiran kasar ne.

Binciken da masana suka yi a Jami’ar Paris ya ce kashi 10 na attajiran kasar za su amfana da kashi 46 na harajin.

Masanan sun yi gargadin cewar matakin zai dada fito da banbancin da ke tsakanin masu hannu da shuni da talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.