Faransa

"Dole ne Isra'ila da Falasdinu su dinke baraka"

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da shugaban Faransa Emmanuel Macron
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Stephane Mahe

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci komawa tattaunawa domin warware rikicin Gabas ta Tsakiya a karkashirin shirin kafa kasar Falasdinu wadda za ta zauna kafada da kafada da Israila.

Talla

Macron ya bayyana haka ne wajen bikin cika shekaru 75 da yadda Faransa ta tura wasu Yahudawa sama da dubu 13 zuwa sansanin 'yan Nazi.

Shugaba Macron ya shaida wa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa, a shirye Faransa ta ke wajen bin matakan diflomasiya domin kawo karshen tankiyar da ake samu.

Macron ya ce, ya zama wajibi Falasdinawa da Yahudawa su zauna tare a karkashin yarjejeniyar zaman lafiya wadda za ta kunshi birnin Kudus a matsayin babban birninsu da kuma mutunta iyakokin juna.

Shugaban na Faransa ya yi wa Netanyahu alkawarin cewar Faransa za ta sa ido sosai wajen ganin kasar Iran ta mutunta yarjejeniyar Nukiliyar da ta kulla da kasashen duniya.

Firaministan Israilan ya bayyana damuwarsa kan gwamnatin Iran da irin matakan da take dauka.

Cikin Israila ya duri ruwa a watan jiya, lokacin da Iran ta harba makamai masu roka kan mayakan ISIS da suka kai harin Tehran wanda ya hallaka mutane 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI