Turai

Kamfanonin Honda da Ford zasu janye motoci sama da miliyan 1

Kamfanonin mota na Ford da Honda sun fara aiwatar da shirin janye motoci miliyan 1.5 saboda matsalar na'urar bai wa direba kariya.
Kamfanonin mota na Ford da Honda sun fara aiwatar da shirin janye motoci miliyan 1.5 saboda matsalar na'urar bai wa direba kariya. consumeraffairs

Kamfanin kera motoci na Ford da takwaransa na Honda, sun shiga jerin kamfanonin  da suke janye dubban motocinsu da suka shiga kasuwannin duniya, dama wadanda aka fara amfani da su, kasancewar suna dauke da laimar bai wa direba, da na gefensa kariya a lokacin hadari, kirar kamfanin Takata na kasar Japan.

Talla

A makwannin da suka gabata ne dai aka gano cewar mafi akasarin na'urorin da suke dauke da laimomin kare direba daga hadari, da kamfanin na Takata ya kera, suna tattare da matsaloli, inda a wasu lokutan, balan balan din da ke fita, ta ke furzar da wasu kananan karafuna tare da kuma fita da karfin gaske, wanda hakan yayi sanadin rasa rayuka akalla 17 a sassan duniya.

A halin yanzu dai kamfanin Honda ya fara aiwatar da shirinsa na janye motocinsa dubu 772,000 a kasar Amurka.

Shi kuwa kamfanin Ford zai janye motocinsa ne akalla dubu 816,000 a yankin arewacin Afrika.

Wani Karin bayani ya ce, zuwa yanzu sama da motoci miliyan 100 masu dauke da na’urar bai direba kariya da Takata ya kera aka janye a duniya, inda a kasar Amurka kadai aka janye miliyan 69.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI