Faransa

Za a rage yawan kudaden tallafi ga marasa galihu a Faransa

Tambarin hukumar tallafin iyali
Tambarin hukumar tallafin iyali PHILIPPE HUGUEN / AFP

Gwamnatin Faransa za ta fara rage yawan kudaden tallafin da take bai wa marasa galihu domin biyan kudin haya da akalla Euro biyar kowane wata.

Talla

Mutane milyan biyar da rabi ne wadanda kowanne ke karbar Euro 230 wannan mataki zai shafa cikinsu kuwa har da dalibai sama da dubu 800.

Wannan mataki ne da tsohuwar gwamnatin kasar ta alkawanta dauka, sannan kuma sabuwar gwmanatin Emmanuel Macron ta aiwatar da shi, a karkashin shirinta na tsimin kudade daga cikin Euro bilyan 18 da take kashewa a shekara domin taimakawa wadanda ba su da muhallai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.