Faransa

Farin jinin Macron ya ragu

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka fitar a yau Lahadi, ya nuna cewa Farin jinin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ragu da kimanin kashi 10 cikin dari, a tsakanin ‘yan kasar, inda a yanzu ya koma kashi 54 daga 64.

Talla

Mashar-hanta dai sun danganta raguwar farin jinin shugaban da da yadda yake fuskantar suka mai zafi, daga ‘yan adawar kasar da ‘yan jaridu, kan matakinsa na zaftare kasafin kudin kasar, da kuma ajiye aikin da daya daga cikin manyan hasoshin sojin kasar ya yi a makon da ya gabata.

Jaridar Journal Du Dimanche, wadda ta udanar da kuri’ar jin ra’ayin, ta kuma ce, goyon bayan tsaurara dokar ta bacin da aka kafa a Faransar domin yakar ta’addanci da Macron yayi, ya taka rawa wajen koma bayan da ya samu, idan akai la’akari da yadda kungiyoyin fararen hula suka rika sukar matakin da cewa, zai bai wa hukumomin tsaron kasar amfani da karfi fiye da kima kan fararen hula.

A watan Yunin da ya gabata ne jam'iyyar Macron ta samu gagarumin rinjaye a zaben 'yan majalisar kasar da ya gudana, lamarin da yasa 'yan adawa a kasar kokawa bisa yadda suka ce hakan zai iya yin tasiri wajen, maida siyasar kasar ta jam'iyya guda, abinda suka ce bai zai haifar da alheri ba da tsarin dimokaradiyyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.