Faransa

Shugaban Faransa Na Shirin Tattauna Rikicin Ukraine Da Takwarorinsa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na shirin tattaunawa da Shugabannin kasashen Rasha, Jamus da Ukraine gobe Littini gameda yadda za su warware rikicin da ake samu a gabashin kasar Ukraine.

Emmanuel Macron tare da Vladmir Putin da Angela Merkel
Emmanuel Macron tare da Vladmir Putin da Angela Merkel RFI
Talla

Wata sanarwa daga fadar Shugaban Faransan na cewa wannan na daga cikin matakai na baya-bayan nan  da manyan kasashen duniyan za su dauka domin kawo karshen wannan rikici.

Shugaban Faransan zai tattauna ne ta wayan talho da Shugaban Rasha Vladmir Putin, da Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko a ci gaba da warware rikici na tun shekara ta 2014 da ya kaiga mutuwar mutane akalla dubu goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI