Poland

Duda ya yi watsi da kudirin sauyi a Poland

Shugaban Poland, Andrzej Duda
Shugaban Poland, Andrzej Duda REUTERS/Kacper Pempel

Shugaban Poland Andrzej Duda ya yi amfani da karfin kujerarsa wajen yin watsi da kudirin sauye-sauyen da Majalisar Dokoki ta amince da shi don bai wa gwamnnati damar nada ‘yan siyasa a mukaman manyan alkalai na kotun kolin kasar.

Talla

Matakin da Majalisar Dokokin ta dauka na gabatar da kudirin samar da sauye-sauyen ya haifar da zanga-zanga na wasu kwanaki a fadin kasar.

Kafin kudirin ya zama doka, wajibi ne shugaban kasa ya rattaba hannu, amma shugaba Duda ya ki amince wa da haka.

Mr. Duda ya ce, ya yi amfani da karfinsa ne wajen yin watsi da dokar bayan ya yi ganawa mai zurfi da kwararru a fannin shari'a a karshen mako, lokacin da dubban ‘yan kasar suka fantsama kan tituna don gudanar da zanga-zanga.

Masu zanga-zangar sun bukaci shugaba Duda da ya yi watsi da kudirin dokar wanda masu caccaka suka bayyana a matsayin barazana ga tsarin Demokradiyya

Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi Poland game da wannan yunkuri, tare da yi ma ta barazanar kakaba ma ta takunkumai a cikin wannan makon muddin ba ta soke kudirin sauye-sauyen ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI