EU

EU ta matsa kaimi kan bai wa baki mafaka a Turai

Wasu daga cikin haure da ke neman mafaka a Turai
Wasu daga cikin haure da ke neman mafaka a Turai ReutersREUTERS/Stefano Rellandini/File photo

Kungiyar Kasahsen Turai ta matsa kaimi wajen ganin kasashen da suka bijire wa yarjejeniyar karbar bakin da suka nemi mafaka a yankin sun karbi adadin da aka ware musu

Talla

Alkalan babbar kotun ta Turai sun amince da yarjejeniyar da kasashen suka kulla cewar, bakin za su samu mafaka ne a kasar da suka fara isa a Turai.

Wannan hukunci na kotun zai shafi kasashe irin su Poland da Hungary da Jamhuriyar Czeh wadanda suka ki karbar bakin a karkahsin wannan yarjejeniya.

Bayan hukuncin, kwamishinan kula da kaurar baki na Turai, Dimitris Avramopoulos ya yi kira ga kungiyar da ta kammala sauya wa baki 'yan gudun hijira 160,000 da ke gabar tekun Bahar Rum matsuguni.

Ya zuwa yanzu baki 24,000 kacal suka samu mafaka a wasu kasahse bayan kammala duba takardunsu.

Kwamishinan ya ce fatarsu ita ce kammala raba bakin da suka rage nan da watan Satumba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI