Faransa
Faransa ta nemi agaji domin kashe wutar daji
Wallafawa ranar:
Sama da mutane dubu 10 ne aka kwashe daga yankin da wutar dajin ta shafa, lura ida yadda gobara ke saurin yaduwa a cikin kwanaki biyu da tashinta.
Talla
Gobarar ta tashi ne a yankin Bormes-les-Mimosas da ke kudancin kasar, yankin da ke jan hankulan masu yawon bude ido sosai a kowace rana ta Allah.
Tuni aka kwashe baki masu yawon bude ido da yawansu ya haura dubu uku daga yankin, yayin da jami'an tsaro da suka hada da 'yan kwana-kwana dubu 4, tare da wasu jiragen saman kashe gobara 19 ke ci gaba da aiki domin murkushe wutar dajin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu