Turai

Kotun Turai ta dawo da Hamas cikin sahun 'yan ta'adda

Ismaïl Haniyeh, jagora a gwagwarmayar Hamas.
Ismaïl Haniyeh, jagora a gwagwarmayar Hamas. SAID KHATIB / AFP

Kotun kolin Turai ta yanke hukuncin da ke tabbatar da kungiyar Hamas ta Falasdinu a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Talla

A shekara ta 2014, kotun Turai ta soke matakin da kasashen yankin suka dauka da ke sanya kungiyar wadda ke iko da yankin Gaza a matsayin ta ta’addanci, inda a wancan karo kotun ta ce an dauki matakin ne ba tare da gabatar da hujjoji ba.

Bayan yanke wancan hukunci na farko, mahukuntan Isra’ila da Amurka sun nuna matukar bacin rai, inda a wannan laraba kotun da ke da babbar cibiyarta a Luxembourg ta dawo da tsohon hukuncin kamar yadda kungiyar ta Turai ta bukata.

To sai dai hukuncin na yau ya bai wa jama’a da dama mamaki, domin a cikin watan satumbar bara lauyoyi da dama da ke kotun ne suka ce yin hakan babban kurkure ne.

A daya bangare kuwa kotun kolin ta Turai ta bayar da umurnin janje sunan kungiyar tawaye Tamil Tigers da ke Sri Lanka daga cikin jerin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI