Turai

Kotu ta umurci gwamnatin Holland ta kula da makarantar Islama

Kotun Kolin kasar Netherlands ta umurci gwamnatin kasar ta dauki nauyin tafiyar da wata makarantar koyar da addinin Islama dake Amsterdam.

Firainistan Holland Mark Rutte
Firainistan Holland Mark Rutte 路透社
Talla

Tun a shekarar 2014 ne mataimakin Ministan ilimi a kasar Sander Dekker ya katse baiwa makarantar kudi bayan da wani daga cikin shugaban gudanarwar makarantar ya bayyana goyan bayan sa ga mayakan kungiyar ISIS.

Sai dai a cewar kotun babu dalilin da zai sa a dauki hukuncin katse baiwa makarantar kudade ganin yadda shugabanin ta suka nesanta kan su da kalaman wancan mutumin wanda kuma tuni aka kore shi daga aiki.

Alkalin kotun ya bukaci ministan ya nemo duk inda kudi yake domin fara baiwa makarantar kafin ranar 1 ga watan gobe da za’a koma karatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI