'Dan Bindiga Ya Kashe Mutane Biyu A Gidan Rawa Na Kasar Jamus
Wallafawa ranar:
A kasar Jamus mutane biyu sun gamu da ajalinsu a wani gidan rawa, wasu mutanen hudu kuma suka jikkata sakamakon hare-harbe a wani gidan rawa kafin wayewar gari yau lahadi.
Wata sanarwa daga ‘yan sandan kasar na cewa wani mutun mai kimanin shekaru 34 ya aikata harbe-harben.
Sanarwar ‘yan sandan na cewa an jikkata maharin a lokacin da ‘yan sanda ke kokarin kama shi yana shirin tserewa don barin gidan rawan amma kuma daga bisani ya mutu a asibiti.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani harin da wani mutun dauke da wuka ya kai shagon saida kayayyaki inda aka sami hasarar rayuka a garin Hamburg.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu