Faransa

Calais: Kotu ta yi watsi da koken gwamnatin kan 'yan ci-rani

'Yan ci-rani na cikin wani yanayi a sansanin Calais da ke Faransa
'Yan ci-rani na cikin wani yanayi a sansanin Calais da ke Faransa DENIS CHARLET / AFP

Wata babbar kotu a Faransa ta yi watsi da koken da gwamnatin kasar ta shigar na kalubalantar yi wa ‘yan ci rani tanadin matsuguni mai inganci a Calais.

Talla

Kotun ta bukaci Gwamnatin Faransa ta samarwa daruruwan ‘yan ci ranin ruwan sha da kuma wasu bukatu na tsabtace muhalli a yankin na arewacin Calais.

A cikin bayanan da kotun ta karanta, ta ce rashin samar da bukatun tamkar cin zarafin bil’adama ne da rashin imani.

Kotun ta ce ‘yan ci ranin na cikin yanayi na rashin ruwan da za su sha har su yi wanka da tsarki da wanke tufafi.

Al’amarin da ya haifar da cututuka da dama da suka shafi fata ga ‘yan ci ranin da dama saboda yadda suke rayuwa a cikin kazanta.

Wasu kungiyoyin sa-kai ne da ‘yan ci ranin suka shigar da karar kan yadda gwamnati ke keta ‘yancinsu na dan adam.

Daruruwan ‘yan ci rani ne dai suka yi sansani a Calais da nufin samun sa’ar tsallakawa zuwa Birtaniya ta barauniyar hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.